Play all audios:
Kungiyoyin da ke dauke da makamai a Siriya sun cimma yarjejeniya a wannan Talata da sabbin hukumomin kasar, wadda ta jibanci ajiye makamai domin bai wa mayakansu aiki a ma'aikatar
tsaro. KARIN BAYANI: Ina makomar Siriya bayan kifar da gwamnati? Kawo yanzu wannan yarjejeniyar ba ta shafi mayakan Kurdawa masu samun goyon bayan Amurka ba, wandanda ke rike da wasu
yankuna da dama a arewa maso gabashin kasar. Sai dai kakakin sabbin hukumomin Siriyar Farhad Chami ya ce za su tattauna kai tsaye da shugabannin mayakan Kurdawan nan zuwa gaba amma ba tare
da tsoma bakin wasu manyan kasashen duniya ba. Wannan yarjejeniya da ke zama wani yunkuri na sake gina Siriya ta biyo bayan ganawar da aka yi tsakanin shugabannin kungiyoyi da ke dauke da
makamai da sabon jagoran kasar ta Siriya Ahmad Al-Charaa wanda ya kifar da Shugaba al-Assad makonni biyu da suka gabata.